SiyasaSabiya
Wani ya kai hari a kan dan sanda a Sabiya
June 29, 2024Talla
Dan sandan dai ya maida martani ta hanyar harbin maharin, ukumomin dukka kasashen biyu sun nuna cewa akwai alamar harin na ta'addanci ne. Ministan Ma'aikatar cikin gida na kasar Ivica Dacic a wata sanarwa ya ce sai da maharin ya harba wa dan sandan wani abu tun da farko kuma abun ya daki wuyan jami'in.Ya kara da cewa dan sandan ya harbe maharin a kokarinsa na kare kai kuma raunuka da ya samu ne suka haddasa mutuwarsa.