Hari a masallacin 'yan Shi'a a Saudiyya
January 29, 2016A kasar Saudiyya mutane uku sun halaka a yayin da wasu 10 suka ji rauni a cikin wani harin da aka kai a wannan Jumma'a a masallacin 'yan Shi'a na Al Ahsa da ke a Gabashin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wasu shaidun ganin da ido dama gidan talabijin na Al Arabiya na kasar ta Saudiyya sun tabbatar da abkuwar harin wanda suka ce an tayar da bam ne a cikin harabar masallacin kafin daga baya kuma maharin ya buda wuta da bindiga.
Ana kyautata zaton dai 'yan sanda sun kama maharin. Wasu hotunan da fayafayin bidiyo da aka wallafa a saman hanyoyin sada zumunta na zamani na nuno 'yan sanda suna harbi a sama domin tarwatsa jama'ar da suka fusata dama kuma gwarwakin wasu mutane ukku kwance gina gina a cikin masallacin.
Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin