Hari a ofishin jakadancin China a Pakistan
November 23, 2018Talla
Wasu 'yan kunar bakin wake su uku na wata kungiyar masu tada kayar baya a Pakistan sun kai hari karamin ofishin jakadancin China dake kudancin Karachi a ranar Juma'ar nan.
Wani mai magana da yawun kungiyar ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Reuters ikrarin cewa su 'yan kungiyar 'yantar da yankin Balochistan sune suka kai harin.
Akalla yan sanda biyu da kuma wani dogari daya sun rasa rayukansu a harin.
Babu tabbas ko akwai wani jam'in kasar China da harin ya ritsa da shi.
China ta yi Allah wadai da harin tare da bukatar hukumomin Pakistan su tabbatar da tsaron lafiyar 'yan China da ke zaune a kasar.