Sulhun Armeniya da Azarbaijan ya dakata
October 12, 2020Yarjejeniyar tsagaita wutar da shugaba Vladimir Putin na Rasha ya jagoranta a birnin Moscow dai ba ta je ko ina ba, domin kuwa a Lahadin da ta gabata sabon fada ya barke tsakanin bagarorin biyu da ke nunawa juna dan yatsa, baya ga zargin harba makamai masu linzami a kan yankunan fararen hula, batun da ya kara ta'azzara rikicin na makonni biyu.
Karin Bayani:Rikicin Armeniya da Azarbaijan ya yi kamari
Harin da Azarbaijan ke zargin dakarun Armeniya da kai wa a birnin Ganja da ke zaman na biyu mafi girma a kasar dai, ya lalata gidajen fararen hula bayan asarar rayukan mutane tara da jikkata wasu gommai ciki har da kananan yara, kasa da sa'o'i 24 da ya kamata ace yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki.
A hukamance dai, a ranar Asabar ne yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki. Sai dai nan take bangarorin biyu suka fara zargin juna da karya ka'idojintata, tun ma kafin aiwatarwa. Ministan harkokin wajen Armeniya Zohrab Mnatsakanyan tun da farko, ya bayyana cewar tattaunawar cimma wannan yarjejeniyar ba ta zo wa bangarorin biyu da sauki ba a birnin Moscow. A cewarsa Armeniya ta nemi kasashen duniya dasu yi la'akari da Nagorno-Karabakh a matsayin 'yantacciyar kasa.
A wannan Litinin din wannan makon ne dai, ma'aikatar harkokin wajen Turkiyyar ta yi tir da harin makamai masu linzami da sojojin Armenia suka kai a Ganja. A karshen mako ne dai ministan harkokin wajen Azarbeijan ya zargi Faransa da goyon bayan Armeniya, a kokarin da ake na warware rikicin yankin na Nagorno-Karabakh.