1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari da wuka a jirgin kasa a Jamus

Abdul-raheem Hassan
November 6, 2021

'Yan sandan sun tsare maharin da ya jikkata mutane da wuka a cikin wani jirgin kasa a jihar Bavariya da ke Kudancin Jamus, mutane uku na cikin mawuyacin hali a gadon jinya.

https://p.dw.com/p/42fVl
Deutsche Bahn | ICE
Hoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

Harin ya faru ne lokacin da jirgin kasa na ICE mai gudun gaske ke tafiya tsakanin biranen Regensburg da Nuremberg, wasu bayanai na cewa mutane uku na cikin mawuyacin hali sakamakon raunin da suka samu a harin.

Jami'an 'yan sanda na cigaba da binciek kan maharin bayan da suka tsare shi, tun a shekarar 2015 kasar Jamus na fuskantar hare-hare da wuka masu alaka da ta'addanci, inda ko a watan Yunin da ya gabata mutane 3 sun mutu wasu 5 sun jikkata a wani hari da wuka a birnin Wuerzberg da ke kudancin kasar.