1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Hari da wuka cikin mota ya jikkata mutane a Jamus

August 31, 2024

Wani hari da wata mata ta kai da wuka cikin motar safa a yammacin Jamus, ya jikkata mutane shida a cewar jami'an 'yansanda. Harin dai ya zo ne mako guda bayan wani da mai neman mafaka ya kai a garin Solingen.

https://p.dw.com/p/4k80x
Wajen da aka kai hari da wuka a birnin Siegen na yammacin Jamus
Wajen da aka kai hari da wuka a birnin Siegen na yammacin JamusHoto: Rene Traut/IMAGO

Matar mai shekaru 32, 'yar kasar Jamus din ce kuma tuni 'yansanda suka kama ta bayan harin da ta kai a garin Siegen.

Bayanai na nuna cewa uku daga cikin wadanda matar ta soka da wukar, na cikin mumunan yanayi na iya rasa rai.

'Yansandan sun ce suna ci gaba da bincike kan musabbabin harin, tare da kore alakarsa da ta'addanci.

Harin dai ya zo ne mako guda bayan wani da mai neman mafaka ya kai da wuka a garin Solingen, wanda ya girgiza Jamus.

Harin na Solingen ya kuma sanya gwamnati tilasta hukumomin tsaro sauya matakan bayar da mafaka ga baki daga ketare.

Haka ma shugaban gwamnati Olaf Scholz ya fito da tsauraran matakan da suka shafi rike wuka a wurare na jama'a a Jamus.

Ko a ranar Talatar da ta gabata ma, 'yansanda sun bindige wani da ya yi yunkurin far wa wani da wukar a kusa da garin Solingen.