SiyasaSudan
Hari kan dam na barazanar haddasa ambaliyar ruwa a Sudan
November 18, 2023Talla
Har yanzu ba a tantance girman barnar da aka yi a madatsar ruwan ba, amma dai tana barazanar haddasa ambaliya ruwa. A baya-bayan nan, fada ya karu a yankin Jebel Awlia wanda ya yi sanadin raba dubban mutane da matsugunansu, a wannan gunduma mai fama da talauci a kudancin lardin Khartum.
A farkon wannan watan ne, dakarun RSF ta mataimakin shugaban kasar Mohammed Hamdan Daglo ta ce ta kama wani sansanin sojoji a yankin. Sannan a cikin 'yan makonnin da suka gabata, an lalata wata gada a babban birnin kasar Khartum tare da lalata wata muhimmiyar ma'ajiyar man fetur a hare-haren da bangarorin biyu ke zargin junansu da kaiwa.