1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hari ya yi sanadiyar gwamman rayukan dalibai

Binta Aliyu Zurmi
June 17, 2023

Akalla gawarwakin mutane 41 ne mahukunta a kasar Yuganda suka ce sun gano, wasu dauke da kuna yayin da wasunsu ke dauke da alama ta harbin bindinga, bayan wani harin ta'addanci na kungiyar ADF.

https://p.dw.com/p/4Shzg
Uganda Mpondwe | Angriff auf Schule
Hoto: AFP

Harin wanda aka kai wata makarantar sakandire ya yi sanadin bacewar mutane 6 kuma ana zargin 'yan bindigar ne suka yi awon gaba da su.

Mafi akasarin wadanda suka hallaka sanidiyyar harin dalibai ne sai dai rahotanni na cewar an samu gawar maigadin makarantar da kuma wasu mutane biyu da ke zaune a gari kamar yadda magajin garin Mpondwe-Lhubiriha ya nunar.

Ya zuwa yanzu dai babu rahoton nasarar kama ko guda daga cikin maharan, sai dai sojoji sun ce sun shige makwabciyar kasar jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango bayan da suka kai hari.

Yuganda dai ta jima da ta aike wa da jami'an sojinta domin taimaka wa Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango yaki da wadannan mahara.

Ko a watan Afirilun da ya gabata 'yan tawayen na ADF sun kai wani mumunan hari a Kwango inda suka kashe mutane 20.