Hari da makaman roka ya halaka mutane a gabashin Ukraine
April 8, 2022Da yake tsokaci game da harin shugaban majalisar EU Charles Michel, yace ya kadu da yadda ya ji Rasha ta kaddamar da harin kan babbar tashar da fararen hula ke amfani da ita don kubucewa hare-haren da ta tsananta a gabashin Ukraine. A yayin da shi kuwa babban jami'in diflomasiyyar kungiyar Josep Borrell, ya baiyana harin da wani yunkuri na toshe duk wata kafa da fararen hula ke tserewa yakin da Rasha take gwabzawa a gabashin Ukraine.
Akalla mutane 35 ne aka hakikance sun gamu da ajalinsu, sakamakon harin rokokin da Rasha tayi kan tashar jirgin, sai dai ma'aikatar tsaron Rasha ta musanta harin tana mai cewa wani yunkuri ne kurum na bata mata suna. Wannan lamarin na zuwa ne a yayin da shugabar kungiyar EU Ursula Von Der Leyen, da babban jami'in harkokin wajen kungiyar ke gudanar da wata ziyarar a birnin Kiev, jim kadan bayan da kungiyar ta kara lafta wasu jerin takunkumai ga Rasha, da ma ware karin makudan kudi Euro miliyan 500 ga Ukraine don kara sayen makaman kare kanta.