1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya halaka gwamman mutane a Shiraz

Mouhamadou Awal Balarabe
October 26, 2022

Akalla mutane 13 ne aka kashe a birnin Shiraz da ke kudancin Iran, a wani hari da makami da aka kai a wurin ibadar 'yan Shi'a. Babu wata kungiya da ta dauki wannan harin ya zuwa yanzu.

https://p.dw.com/p/4Iiwh
Wadanda suka rasa rayukansu a harin Shiraz na IranHoto: Tasnim Agency

Hukumomin Iran sun zargi 'yan kasashen waje da kai wannan hari da ya ritsa da mace daya da yara biyu. Sai dai shugaban hukumar shari'a na yankin, Kazem Moussavi, ya ce an kama mutum daya daga cikin wadanda suka kai harin.

 Dama dai a farkon watan Afrilu, wani matashi dan asalin kasar Uzbekistan ya daba wa wasu malaman Shi'a biyu wuka har lahira, tare da raunata na uku a harabar ubbaren Imam Reza da ke Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran. Amma an rataye maharin tun watanni hudun da suka gabata bayan da aka same shi da laifin da aka tuhume shi da aikatawa.