SiyasaTarayyar Rasha
Harin Rasha ya halaka mutane 14 a Ukraine
March 15, 2024Talla
Wani harin da Rasha ta kaddamar da makamai masu linzami ya halaka mutane 14 a garin Odesa na kudancin kasar Ukraine, kana wasu mutane kimanin 20 suka jikata kamar yadda masu aikin agajin gaggawa suka tabbatar a wannan Jumma'a.
Galibin makaman da aka harba sun fadi kan gidajen fararen hula abin da ya haifar lalata motoci da da bututun kai gas gidaje. Fiye da shekaru biyu da suka gabata kasar ta Rasha ta kaddamar da kutse kan kasar Ukraine lamarin da ya haifar da martani daga bangarorin daban-daban musamman manyan kasashe na Yammacin Duniya da suka dauki matakin taimakon Ukraine fita daga wannan kangi.