Al-Shabaab ta kai hari
May 14, 2019Talla
Harin farko ya faru ne a gundumar Warta-Nabadda inda wani dan kunar bakin wake ya tayar da nakiyar da ke jikinsa inda ya kashe mutane shida tare da jikkata wasu 30.
A yayin da nakiya ta biyu ta fashe a lokacin da jerin gwanon tawagar sojin kasar ke sintiri a yankin Afgoye, har sojoji uku suka mutu wasu hudu kuma suka tsira da munanan raunuka, kamar yadda wani jami'in dan sandan Somalia Ali Hassan ya tabbatar.
Tuni dai kungiyar ta Al-Shabab ta tabbatar da daukar alhakin kai harin ta kafar Rediyonta. Al-Shabab din dai ta kara tsaurara hare-haren ne a cikin wannan wata na Ramadan inda ta ke nufar Otal-Otal da shingen jami'an tsaro da ma gine-ginen gwamnati.