1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ƙunar bakin wake a Pakistan ya halaka mutane 50

Ibrahim SaniDecember 21, 2007
https://p.dw.com/p/Celk

Wani ɗan ƙunar baƙin wake a Pakistan ya yi ajalin mutane kusan 50. Bom ɗin a cewar rahotanni ya tashi ne a lokacin da ake tsakiyar Sallah, a cikin wani masallaci dake arewa maso yammacin ƙasar. A lokacin da bom ɗin ya tashi, akwai masallata sama da dubu a cikin Masallacin. Wani daya ganewa idonsa ya shaidar da cewa, ɗan ƙunar bakin waken na bayan tsohon ministan harkokin wajen ƙasar ne, a dai dai lokacin da bom ɗin ya tashi. Rahotanni sun ce da alama an kai harin ne da zummar halaka Mr Mr Aftab Ahmed, to amma bayanai sun tabbatar da cewa babu abinda ya sami tsohon ministan. Wannan dai shi ne karo na biyu da ake ƙoƙarin halaka tsohon ministan, a tsawon watanni takwas. Mr Aftab Ahmed dake zaman na hannun daman shugaba Musharraf, a yanzu haka na takarar kujerar majalisar dokokin ƙasar.