Somaliya: Harin al Shabab ya halaka sojoji 27
July 23, 2018Talla
Rahotanni na nuni da cewa, maharan sun yi anfani da wata karamar mota da suka cika da bama-bamai wajen kai harin na wannan Litinin. Jim kadan da kai harin, kungiyar ta bakin kakakinta Abdiasis Abu Musab ta fitar da sanarwa, inda a ciki ta dauki alhakin kai harin tare da fadin alkaluman sojojin da ta kashe.
Babu bayani daga bangaren hukumomin kasar kan harin da ikirarin kungiyar. A watan Yunin da ya gabata, mayakan kungiyar sun kai hari a sansanin sojin inda suka raunata sojoji bakwai. Al Shabab na ci gaba da gwagwarmaya da makamai don ganin ta kawar da gwamnatin da ke kan mulki don kafa ta-ta gwamnati bisa shari'ar addinin Islama.