1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Amirka ya hallaka mutane 27 a Siriya

Ramatu Garba Baba
August 21, 2017

A kasar Siriya mutane akalla 27 suka salwanta a wani hari da dakarun kawance da Amurka ke jagoranta ta kai a yankin birnin Raqa da ke karkashin ikon 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/2iZet
Syrien Provinz Rakka US-Soldaten Spezialkräfte
Hoto: Getty Images/AFP/D. Souleiman

A kasar Siriya mutane akalla 27 suka salwanta a wani hari da dakarun kawance da Amurka ke jagoranta ta kai a yankin birnin Raqa, dakarun sun kaddamar da harin a birnin da 'yan tawaye ke rike da su da zummar fatatakar mayakan, babban jami'i na kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syria "Observatory for Human Rights" Rami Abdel Rahman ya ce duk wadanda suka mutu a harin fararren hula ne ciki kuwa har da kananan yara bakwai.

A cewar kungiyar baya ga wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin na ranar Lahadi, fararren hula fiye da dari daya ne kuma suka mutu a hare-haren da dakarun kawance suka kai a birnin na Raqa a makon da ya gabata, Dakarun kawancen da ke kokarin kawo karshen kungiyar IS a kasashen Siriya da Iraki sun ce suna daukar matakai don ganin an kauce wa samun asarar rayukan fararren hula.