Harin bam a Pakistan
November 1, 2007Talla
Akalla mutane 8 ne suka rasa rayukansu wasu kuma 40 suka samu raunuka a cikin wani harin kunar bakin wake da aka kai akan wata bus ta rundunar sojin ruwa ta kasar Pakistan kusa da birnin Sargodha dake tsakiyar kasar.wannan shine harin kunar bakin wake na biyu da aka kai cikin wannan mako.wani mai magana da yawun rundunar ruwa ta kasar yace dan kunar bakin waken ya kara mashin da yake kai ne jikin bus din dake dauke da jamian soji zuwa sansaninsu a yankin.