1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam a Yuganda

July 13, 2010

Yanzu dai ta tabbata Ƙungiyar Alshabab ce ta kai harin ta'addanci a Yuganda, harin da kuma ya sa mutane da yawa suka mutu.

https://p.dw.com/p/OIB2
Waɗanda suka ji rauni a harin YugandaHoto: AP

Jami'in tsaro a ƙasar Yuganda sun sanar da samun wasu bama bamai da aka ɗana waɗan da basu tashi ba, kwana guda bayan tagwayen hare-haren bam, waɗanda suka hallaka aƙalla mutane 74, wasu kimanin 80 suka jikkata, izuwa yanzu dai 'yan sanda sun kama mutane dayawa da ake zargi da kai harin.

Tun lokacin da harin ya faru dai, hankali ya koma ga ƙungiyar tsagerun Alshabab, dake dauke da makamai a Somalaiya. Sa'o'i bayan harin ƙungiyar da kanta tafi afili ta amince da kai wannan harin, inda tace kuma za ta ci gaba da kaiwa kadarorin Yugunda hari a duk inda suke a duniya. Wannan ƙungiyar dai tana mai cewa martanine ga Yuganda bisa tura sojojinta a Somaliya, inda Alshaba ke cewa daukar fansa ne da bisa hallaka yara da tsaffi wanda dakarun Yuganda ke yi. Hakan sa 'yan adawa a ƙasar ƙira ga gwamnatin da ta janye dakarunta daga Somaliyan. to ama mutane kamar Yusuf Kiranda jam'i a cibiyar agaji ta Korrad Adenauer dake Kampala na masu ra'ayin cewa hakan zai kasance gurguwar shawara.

"Ina fatan kada wannan mummunan matakin 'yan ta'adda ya kasance sandin da Yugunda za ta pice daga Somaliya. Kamar yadda a yanzu Yugunda take ganin matakin ruddunar kiyaye zaman lafiya da ta tura, shine na samar da tsaro a nahiyar"

Ƙungiyar Alshabab dai ta gargaɗi duk wata ƙasa da ta ke da dakaru a Somaliya to ta kuka da kanta. Kakakin ƙungiyar Sheikh Ali Muhammed yace Burinda ma ta ɗauke, samarin da ta kai Mogadishu, idan ba haka ba, to Bujumbura ma za ta fiskanci irin hare-haren bama bamai. Domin yace itama Yugunadar sun gargaɗe ta kafin kai wannan harin amma ta yi watsi da hakan. Ganin yadda aka kasa kawar da Alshababa, da tabbatar da kare gurguwar gwamnatin ƙasar Somaliya, shine ma yasa ƙasashen yakin dake ƙungiyar IGAD, suka amince da tura ƙarin dakru 2000. Anette Weber jami'a ce a cibiyar binciken fannonin siyasa dake Berlin.

"Bayan haka ne Alshabab ta fara barazana ga ƙasashen dake da sojoji a Somaliya, wato Ruwanda da Burundi. Tana mai cewa za ta tura maharnta su riƙa kaiwa al'ummomin waɗannan ƙasashen hari. Idan kuwa ta tabbata cewa Alshabab ce ta kai hari a Yuganda, to sai muce ɗaukacin yankin gabashin Afirka yana cikin hatsari, na faɗawa cikin rashin zaman lafiya, ta ƙaruwar hare haren ta'addanci"

Yanzu haka dai ruddunar kiyaye zaman lafiya ta Somaliya wanda ke ƙarƙashin Tarrayar Afirka, tana da sojoji dubu 5000, akasarinsu daga ƙasashen Burundi da Yuganda.

Nan take bayan kai hari aka samu martane da yin Allah wadai, kama daga Shugaban Amirka Barack Obama da ministan harkokin wajen Jamus, da MDD. To ko hakan yana nufin ƙasashen duniya za su kai ɗauki na samar da zaman lafiya, a wannan ƙasar da yaƙi ya ɗai ɗaita, yanzu dai lokacin ne kawai zai faɗa.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Adrian Kriesch

Edita: Umaru Aliyu