1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Harin bam ya haddasa mace-mace a Istanbul

Binta Aliyu Zurmi MAB
November 13, 2022

Akalla mutane shida sun mutu a Istanbul yayin da wasu sama da 50 suka jikkata sakamakon fashewar bam a titin da ke fama da kai komon jama'a musammam baki 'yan yawon bude ido.

https://p.dw.com/p/4JSci
Kwararru na bincike bayan harin bam a Istanbul na TurkiyyaHoto: Kemal Aslan/REUTERS

Ma'aikatan agaji na ci gaba da bai wa wadanda suka jikkata a harin na Istanbul taimakon gagawa. Sai dai ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan harin. Amma shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan ya alakanta harin da ta'addanci, yana mai shan alwashin daukar matakin doka a kan wadanda ke da alhakin shi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Turkiyya ke samun irin wannan fashewar bam a kwaryar manyan birane ba. Ko a shekarar 2015 da kuma 2017 kungiyar IS da ke gwagwarmaya da makamai ta kaddamar da munanan hari da har yanzu ake gudanar da bincike a kai.