1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam ya kashe mutane da dama a Kabul

Gazali Abdou Tasawa
July 24, 2017

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin da aka kai a birnin Kabul na Afganistan  da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 35 a sakamakon tashin wani bam da aka dana ga wata mota a wata unguwar mabiya mazhabin Shi'a. 

https://p.dw.com/p/2h2GM
Afghanistan Kabul Autobombe
Hoto: Reuters/TV

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin da aka kai a birnin Kabul na Afganistan  da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 35 ya zuwa yanzu, a yayin da wasu sama da 40 suka ji rauni a sakamakon tashin wani bam da aka dana ga wata mota a wata unguwar mabiya mazhabin Shi'a a wannan Litinin. 

Kakakin ofishin ministan ma'adanai na kasar ta Afganistan Najib Danish ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa da misalin karfe bakwai na safe ne motar da ke dauke da bam din ta kutsa a guje ta kai karo kan wata motar bus da ke dauke da ma'aikatan ofishin ministan ma'adanai. 

Wasu shaidun gani da ido sun ce wani bakin hayaki ya turnuke zuwa sama bayan tashin bam din kana sun ce akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su daliban jami'a ne da ke shirin tafiya rubuta jarabawar kammala karatun shekara da kuma jami'an tsaro da ke gadin gidajen wasu 'yan majalisa mabiya tafarkin Hazara wani reshe na mazhabin Shi'a.