Harin kunar baƙin wake a Pakistan
July 14, 2007Talla
A ƙalla sojojin Pakistan 18 suka rasa rayukan su wasu da dama kuma suka sami raunuka, a yayin wani harin ƙunar baƙin wake. Ɗan ƙunar baƙin waken ya kutsa da motar sa dake ya ɗauke da nakiyoyi inda ya afka wa jerin gwanon motocin sojoji a yankin Waziristan dake kusa da kan iyaka da Aghanistan, yankin da ya yi ƙaurin suna wajen ɗauki ba daɗi tsakanin sojoji da mayakan sa kai na ketare. An danganta harin da afkawa masallacin Lal Masjid da sojojin Gwamnatin Pakistan suka yi a Islamabad a wannan makon. Ana dai baiyana fargar cewa masu tsatsauran raáyin addini ka iya ƙaddamar da jihadin juyin juya halin Islama a ƙasar ta Pakistan. A yanzu dai gwamnatin ta tura dubban sojoji zuwa yankin na Waziristan domin tabbatar da harkokin tsaro.