Kungiyar Taliban ta kai hari a ofishin jakadancin Turkiya
February 26, 2015Talla
Rahotanni sun nunar da cewa tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin bam din da ya tashi a kofar ofishin jakadancin Iran, inda ta ce ta kudiri kai harin ne a kan ayarin motocin wasu 'yan kasashen ketare. Mataimakin ministan cikin gida na kasar ta Afghanistan Mohammad Ayub Salangi ya tabbatar da faruwar al'amarin. Jami'an 'yan sandan kasar sun ce daya daga cikin wadanda suka rasa rayukansu dan kasar Turkiya ne kana gudan kuma dan Afghanistan din ne da ya zo wucewa.