1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake a arewacin Kamaru

Salissou BoukariJune 30, 2016

A kalla mutane 11 ne suka rasu sakamakon wani harin kunar bakin wake da tuni aka dora alhakinsa a kan mayakan Boko Haram a yankin arewacin kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/1JGmC
Kamerun Anschlag in Maroua
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Rahotanni daga birnin Yaounde na kasar Kamaru na cewa, harin dai ya faru ne kusa da wani masallaci a garin Djakana da ke Arewacin kasar, inda bayan da suka yi sallah mutane suka zauna a karkashin wata runfa bayan shan ruwa da yammacin ranar Laraba, a a daidai wannan lokaci ne wani yaro matashi dan kunar bakin wake ya tarwatsa kanshi tare da hallaka mutanen 11 yayin da wasu guda hudu suka samu raunuka.

Tun dai bayan da aka ci karfin mayakan na kungiyar Boko Haram, suka kaddamar da wani sabon salo na kai hare-haren kunar bakin wake ta hanyar amfani da yana kanana maza ko 'yan mata inda harin ya koma ga baki daya a halin yanzu kan al'umma fararan hula.