Harin kunar bakin wake a Yemen
October 9, 2014Talla
Wannan hari dai ya zo ne a dai dai lokacin da ake fuskantar yanayi na rikicin siyasa a wannan kasa, inda firaministan da aka zaba a ranar Talata da ta gabata Ahmed Awad ya yi murabus, bayan da bangaran 'yan Shi'a suka yi watsi da nadin da aka yi masa, kuma shi ne hari mafi muni da aka fuskanta a birnin na Sanaa tun bayan na watan Mayu a shekara ta 2012 da aka fuskanta, da yayi sanadiyar rasuwar daruruwan mutane wanda kuma kungiyar Al- Qaida ta dauki alhakinsa a wancan lokaci. 'Yan tawayen 'yan Shi'a na kasar ta Yemen, na rike da birnin na Sanaa tun daga ranar 21 ga Satumba da ya gabata.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo