1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kyamar baki bakaken fata a Italiya

Salissou Boukari
February 4, 2018

Wani dan kasar Italiya ya buda wuta kan wasu baki bakar fata guda shida cikinsu har da mace guda a birnin Macerata, yayin da ake tsakiyar yakin neman zabe a shirin da ake na fuskantar zaben 'yan majalisar dokoki a kasar.

https://p.dw.com/p/2s689
Italien Schießerei in Macerata
Hoto: picture-alliance/ANSA/G. Picchio

A cewar ministan cikin gidan kasar ta Italiya Marco Minniti, wanda ya yi harbin yana da akida ta wariyar launin fata, kuma mutanen shida sun kasance 'yan kasar Mali, Ghana da kuma Najeriya. Magajin garin birnin na Macerata Romano Carancini, ya ayyana dokar hana fita a lokacin harbe-harben wanda tsawon awoyi biyu ya haddasa rudani a tsakanin al'umma a wannan birni da ke da al'ummar da yawanta ya kai mutun dubu 43. Matashin da ya kai harin mai suna Luca Traini, dan shekaru 28 da haihuwa,  ya shaida wa 'yan sandan da suka kama shi cewa Italiya ta 'yan Italiya ce.

Bayan wani taron gaggawa da ya jagoranta da yammacin ranar Asabar, ministan cikin gidan kasar ta Italiya ya ce harbe-harben akida ce ta masu tsauraran ra'ayi na kyamar baki, inda ya ce babban abun da ya hada wadanda aka harben shi ne launin fatarsu.