EU ta damu da harin Rasha a Zaporizhzhia
March 9, 2023Talla
Katsewar wutar lantarkin yana nufin a yanzu sai an rika amfani da man diesel domin sanyaya na'urori a tashar wadda ke fuskantar hadari a cewar babban jami'in harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Joseph Borrel. Ya ce wannan babban keta matakan kariya ne Rasha ta aikata.
Tashar makamashin nukiliyar ta Zaporizhzhia ita ce mafi girma a nahiyar Turai. Joseph Borrel ya ce Rasha na kokarin jefa daukacin nahiyar Turai cikin hadari
Harin da aka kai kusa da tashar nukiliyar ya faru ne sakamakon wasu sabbin hare hare da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine wanda ya hallaka akalla mutane tara da kuma katse wutar lantarki a fadin kasar.