1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Rasha ya kashe mutane uku a Odesa

Abdullahi Tanko Bala
June 14, 2023

A kalla mutane uku sun rasu wasu goma sha uku kuma suka jikkata a wani harin makami mai linzami da Rasha ta harba birnin Odesa mai tashar jiragen ruwa a kudancin Ukraine

https://p.dw.com/p/4SXk8
Hare haren Rasha a birnin Odessa
Hoto: State Emergency Service of Ukraine/REUTERS

Rasha ta harba makamai masu linzami guda hudu daga wani jirgin ruwa a kogin Bahar Aswad a cewar wani mai magana da yawun rundunar soji a yankin. Ya ce harin ya fada wani wurin ajiyar kaya inda ya hallaka mutum uku da jikkata wasu mutanen bakwai. Wasu mutanen shidda kuma sun sami raunuka bayan wani hari ta sama a rukunin kantuna da gidaje a tsakiyar birnin na Odesa.

Harin ya zo ne kwana guda bayan harin wasu makamai masu linzami da aka kai mahaifar shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy inda mutane goma sha daya suka rasu.

Birnin Odesa birni ne da 'yan yawon bude idanu suke kai ziyara daga Ukraine da kuma Rasha kafin shugaba Vladimir Putin ya kaddamar da hari a watan fabrairun bara.

A watan janairu hukumar kula da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta baiyana Odesa a matsayin birnin tarihi na duniya da ke fuskantar hadari.