1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin rokoki a Abbottabad na Pakistan

January 27, 2012

Wasu mutane da ba a san ko su wane ba sun harba rokoki tara a wata cibiyar sojoji da ke kusa da inda aka kashe Osama bin Laden a bara a arewacin Pakistan.

https://p.dw.com/p/13rJ8
HANGU, May 26, 2011 (Xinhua) -- A man stands next to his house destroyed in a suicide blast in northwest Pakistan's Hangu on May 26, 2011. At least 25 people including an unknown number of policemen were killed and over 50 others injured in a suicide car bomb attack that took place Thursday evening in Hangu, some 70 kilometers southwest of Peshawar, reported local Urdu TV channel Samaa. (Xinhua/Stringer) (zw) XINHUA /LANDOV
Harin ta'addanci a Pakistan.Hoto: picture alliance/landov

Hukumomin birnin Islamabad na Pakistan sun bayyana cewa an harba rokoki tara a cibiyar horas da jami'an tsaro, wanda ke kusa da gidan da sojojin ƙundunbala na Amirka suka kashe Osama bin Laden a watan mayu 2011. Babu ko da mutun guda da ya ji rauni. Sai dai biyu daga cikin rokokin sun lalata wani ɓangare na ginin kwalejin kana wasu kuma sun faɗa cikin wata gona da ke daura da cibiyar ta Abbottabad da ke arewacin Pakistan. Wani babban jami'in 'yan sanda ya nunar da cewa daga tsaunukan da ke kewaye da garin ne aka harbasu.

Har ya zuwa yanzu dai, hukumomin ba su gano waɗanda suka harba rokokin ba. Sai dai ƙungiyar al-Ƙaida da kuma ƙungiyar Taliban ta Pakistan sun sha alwashin ɗaukar fansa game da kashe shugaban ƙungiyar ta al-ƙa'ida da aka yi. A ranar biyu ga watan mayu ta shekarar da ta gabata ce, sojojin ƙudunbalan Amirka suka kutsa gidan da Osama Bin Laden ya ke ɓoye, tare da hallaka shi mutumin da Amirka ta shafe shekaru ta na nema ruwa a jallo.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala