1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta tuhumi Iran da kaiwa Saudiyya hari

Zulaiha Abubakar
September 15, 2019

Fadar mulkin Amirka ta White House ta ce akwai yiwuwar Shugaba Donald Trump ya iya ganawa da takwaransa na Iran Hassan Rouhani duk zargin Iran din da Amirkan ta yi da hannu a harin da aka kai matatar man Saudiyya.

https://p.dw.com/p/3Pe0r
Saudi-Arabien Feuer in der Aramco-Ölaufbereitungsanlage in Abkaik
Hoto: Reuters/Stringer

Tun da fari sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya dora alhakin hare-haren da aka kaiwa Saudiyya din a dan tsukin nan wanda yawansu ya ki 100 kan kasar ta Iran.

Da ya ke mai da martani game da wannan zargi shugaban dakarun tsaron juyin juya hali a kasar ta Iran Janar Amir Ali Hajizadeha ya gargadi Amirka da cewar jami'an rundunar, sun shirya tsaf don kai harin ramuwar gayya da makamai masu linzami a dukkan sansanin sojin Amirka da ke yankin Gabas ta Tsakiya da zarar Amirka ta kai hari matatun man Iran.

Da yake tsokaci kan wannan batu, ministan harkokin kasashen wajen Birtaniya Dominic Raab ya yi Allah wadai da harin da a ka kaiwa matatar mai a Saudiyya, tare da danganta al'amarin da yunkurin durkusar da hada-hadar mai tsakanin kasashen duniya. Wannan danbarwa dai na zuwa ne yayin da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ke gabatowa.