Harin ta'addanci a ƙasar Pakistan
January 15, 2011Aƙalla mutane 17 suka hallaka a wani sabon rikicin siyasa da ya ɓarke a Karachi da ke zama cibiyar cinikayyar ƙasar Pakistan. Wasu 'yan tayar da ƙayar baya da ba akai ga tantance ba su ne suka buɗe wata akan gungun mutane a unguwanni daban daban na garin da ke kudancin Pakistan. Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a wannan hari har da wani ɗan jarida da ke yi wa tashar talabijin ƙasar farautar labarai.
Masharhanta da kuma jami'an tsaron Pakistan na dora alhakkin hare-haren da birnin Karashi ke fiskanta kan jam'iyun MQM da kuma ANP da ke gaba da juna. Ministan da ke kula da harkokin cikin gida na Pakistan ya isa birnin na karashi domin yin nazarin hanyoyin da za a bi wajen ɗinke ɓarakar da ke tsakanin jam'iyun biyu, tare da magance hare-haren ta'addaci da yankin ya yi ƙaurin suna akai.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman