Harin ta'addanci a London a gaban majalisar dokoki
March 22, 2017Talla
Wani mutum dauke da wuka ya kai hari a gaban ginin majalisar dokokin Birtaniya,shugaban majalisar wakilai David Lidington ya sanar da cewar 'yan sanda sun harbe mutumin.
'Yan sanda sun ce mutane uku ne kawo yanzu suka mutu kana wasu 20 sun jikkata.
Shaidun gani da ido sun ce sun ga wani mutum da ya taho a guje na kokarin tsallaka shinge da ya kewaye majalisar dokoki wanda daga bisani ya cakawa wani dan sandar wuka.
Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar Brussels ke juyayin cika shekara guda da harin ta'addancin da ya kashe mutane a 32 a filin jiragen sama da ke Brussels.