1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Harin ta'addanci a Jamhuriyar Benin ya hallaka sojojinta 7

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 6, 2024

Harin na kwanton bauna ne daga kungiyoyin da ke da alaka da al Qaeda a IS, a yankin Tanguieta

https://p.dw.com/p/4gjt8
Hoto: Sia Kambou/AFP

Wani harin ta'addanci a Jamhuriyar Benin ya hallaka sojojin kasar 7, a wurin shakatawa da yawon bude ido na Pendjari da ke arewacin kasar, kamar yadda hukumokin tsaron kasar suka sanar a Alhamis din nan.

Karin bayani:An hallaka masu zanga-zanga a kasar Benin

Majiyar tsaron ta ce harin na kwanton bauna ne daga kungiyoyin da ke da alaka da al Qaeda a IS, a yankin Tanguieta mai kusanci da iyakar Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, wadanda ke fama da hare-haren ta'addanci.

Karin bayani:'Yan bindiga sun halaka mutane a iyakar Jamhuriyar Benin da Nijar

Ko a cikin watan Afirilun da ya gabata ma harin ta'addancin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku, a kusa da iyakar Benin din da Jamhuriyar Nijar.