SiyasaAfirka
Harin ta'addanci a kasar Mali ya hallaka mutane 40
July 3, 2024Talla
Wani harin ta'addanci a arewacin kasar Mali ya hallaka mutane 40, kamar yadda magajin garin Bankass Moulaye Guindoin ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho.
Karin bayani:Mali: 'Yan bindiga sun kashe mutane a Mopti
Harin ya faru a kauyen Djiguibombo na yankin Mopti mai fama da hare-haren 'yan ta'adda masu alaka da al Qaeda da IS, a daidai lokacin da ake tsaka da gudanar da biki, kuma yawancin mamatan maza ne.
Karin bayani:MDD na fargabar fantsamar rikicin kasashen Sahel zuwa makwabta
Dubban mutane ne dai suka rasa rayukansu tun bayan barkewar tashe-tashen hankula a kasashen yankin Sahel, da suka hada da Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, wanda ya janyo juyin mulkin sojoji a kasashen.