Wani dan kunar bakin wake ya kai hari a Masar
January 22, 2016Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da jami'an tsaro da kuma 'yan sanda. Mutane da dama dai sun jikkata yayin wannan hari da ke zuwa kwana guda gabanin bikin tunawa da juyin-juya hali na kasar, wanda wasu magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta kasar suka sha alwashin fitowa su gudanar da zanga-zanga duk kuwa da ikirarin da jami'an tsaro suka yi na yin amfani da dokar hana zanga-zangar da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a baya-bayan nan domin dakile masu yunkurin gudanar da zanga-zangar. Wani shaidan gani da ido ya shaidawa manemama labarai cewa:
"Munga wani mutum bom din ya tashi da shi yana kwance a kan gadonsa, daga bisani sai muka ga naman mutane ya warwatsu a ko ina."
Tuni dai jami'an 'yan sandan kasar suka dora alhakin kai harin a kan kungiyar 'yan uwa Musulmi da aka haramta a kasar.