Harin ta'addanci ya halaka sojoji a Burkina Faso
September 25, 2022Rahotanni daga Ouagadougou na cewar wani harin ta'addanci ya hallaka jami'an tsaro hudu a gabashin kasar Burkina Faso a yayin wani aikin sintirin tsaro da suke yi tsakanin garuruwan Sakoani da Sampieri a yankin Tapoa mai makwabtaka da kasashen Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin.
Harin kwantan baunar na 'yan ta'addan ya halaka sojoji biyu da kuma wasu biyu daga tawagar masu rajin kare kasarsu ta kungiyar VDP.
Wata majiya ta tabbatar da samu asarar rayuka a bangaren 'yan ta'addan a gumurzun da suka yi.
Tun a shekarar 2015 Burkina Faso ke fama da da mayankan da ke ikirarin jihadi, wanda ya yi sanadiyar rayukan dubban mutanen tare ma da raba sama da miliyan biyu da matsugunansu.
Ire-iren wadannan hare-haren a kan jami'an tsaro da farafen hula da masu bada agaji na kara karuwa a kasar da ke fama da matsalar tsaro da kuma ta shugabanci.