Harin ta'addanci ya hallaka gomman rayuka a Mali
September 19, 2024Talla
Wani harin ta'addanci da aka kai a tsakiyar kasar Mali, ya yi sanadin mutuwar sama da 70 wasu kimanin 200 kuma suka jikkata, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro suka tabbatar.
Hari ne dai da 'yan ta'addan suka kai sansanin horar da jami'ai da ke ladabtar da sojoji da ke a birnin Bamako.
Tun da fari dai wasu alkaluman sun nunar da cewa mutum 77 ne suka mutu a lamarin wasu kuma akalla 255 suka jikkata.
Hari ya kuma zo ne bayan da gwamnatocin mulkin sojin kasashen Sahel uku wato Malin da Nijar da Burkina Faso suka cika shekara guda da kafa kungiyar nan ta AES bayan bayyana ficewarsu daga kungiyar ECOWAS a farkon wannan shekara.
Kasashen uku sun koma karkashin mulkin soji ne tun bayan juyin mulki da ya faro a 2020 a yankin yammacin Afirka.