Taho mu gama a sansanin sojan Burundi
December 11, 2015Talla
Mazauna birnin Bujumbura sun ji karar bindigogi da kuma ta abubuwa masu fashewa a yayin artabu tsakanin jami'an sojojin kasar da kuma 'yan bindigar da suka kai harin. A wani jawabi da ya yi a gidan radiyon kasar, kakakin rundunar sojojin Kanal Gaspard Baratuza ya bayyana cewa kawo yanzu sun cafke maharan guda 20, kana daga cikinsu akwai wani wanda ya samu raunuka da a yanzu haka yake karbar magani a asibitin sojojin. Baratuza ya kara da cewa akwai wasu sojoji guda biyar da suka samu raunuka a yayin bata kashin.