Harin ƙunar baƙin wake a Pakistan
September 2, 2010Aƙalla mutane 31 sun rasa rayukansu a birnin Lahore na gabashin Pakistan, a lokacin da wasu 'yan ƙunar baƙin wake suka ƙaddamar da jerin hare-hare a wurin ibada na mabiya mazhabar Shi'a. Wasu ƙarin mutane 180 sun ji rauni bayan da waɗanda aka danganta da 'yan taliban suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a cikin cunkoson jama'a da suka kai 35.000 da ke shirin yin buɗa baki.
Haren-haren ƙunar baƙin wake har 400, da suka salwantar da rayukan mutane 1.600 'yan Taliban suka ƙaddamar a ƙasar ta Pakistan cikin shekaru ukun nan da suka gabata. Suna zargin gwamantin Islamabad da mara wa Amirka baya a abin da suka kira yaƙi da addinin musulunci.
Ƙasar Amirka ta sanya ƙungiyar Taliban ta Pakistan a hukumance a cikin jerin ƙungiyoyin ta'adda da ta keman murkushe su. Wannan ƙungiya ta 'yan Taliban ta Pakistan, ta ɗauki alhakin harin da ya ci tura a dandali shaƙatawa na Times Squares da ke birnin New-York.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Halima Balaraba Abbas