1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin siyasa a Pakistan na ci gaba da zafafa

Ibrahim SaniNovember 14, 2007
https://p.dw.com/p/CDoH

Shugabar adawa ta Pakistan, Benazir Bhutto ta ce sanarwar zaɓe da shugaba Musharraf ya yi, abu ne da zai taimaka wajen komar da ƙasar tafarki na Dimokruɗiyya. To sai dai duk da haka a cewar Benazir Bhutto, zai yi wuya kwalliya ta biya kuɗin sabulu, idan ƙasar na ci gaba da kasancewa a cikin dokar ta ɓaci. Halin da ake ciki a ƙasar yanzu a cewar shugabar adawar, ba zai yiwu aci gaba da yaƙin neman zabe ba, a sabili da kasancewar dokar ta ɓacin.Tuni dai Mr Musharraf ya ce ya kafa dokar ta ɓacin ne, bisa hali na rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta.To sai dai ya zuwa yanzu Mr Musharraf bai faɗi lokacin da za´a kawo karshen dokar ta ɓacin ba a ƙasar.Tuni dai Amirka ta bakin sakatariyar harkokin wajen ƙasar, ta yaba da wannan mataki na Mr. Musharraf.Condoleezza Rice ta ce,Muhimmin abu a nan shi ne za´a gudanar da zaɓe, kuma Mr Musharraf zai ajiye kakinsa na soji,waɗannan abubuwane da zasu mayar da ƙasar turbar Dimokruɗiyya.