1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zabe

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
November 1, 2024

Kalamun 'yan takarar yakin neman zabe Kamala Haris da Donald Trump kan bakin haure da 'yancin mata na yamutsa hazo a yayin da aski yazo gaban goshi a gangamin yakin neman zaben Amurka.

https://p.dw.com/p/4mTTK
Harris da Trump na mayar da martani mai zafi a gangamin yakin neman zaben Amurka
Harris da Trump na mayar da martani mai zafi a gangamin yakin neman zaben AmurkaHoto: Matt Bishop/Sipa USA/Charlie Neibergall/AP/Picture Alliance

Manyan 'yan takara a babban zaben Amurka na kace-nace kan batun bakin haure da 'yancin mata, a daidai lokacin da aski yazo gaban goshi a gangamin yakin neman zaben kasar da za a gudanar nan da kwanaki biyar masu zuwa. Kamala Harris ta jam'iyyar Democrat, ta ja daga da abokin karawarta da ke neman kome kan kujerar mulki ta fadar White House Donald Trump, kan muhimman batutuwan da ke yamutsa hazo a gangamin yakin neman zabe a yayin tarukan da suka gudanar na samun kaso mafi rinjaye na masu kada kuri'a a manyan jihohi. A Nevada da ke kudanci, 'yar takara Kama Haris ta caccaki abokin hamayarta Donald Trump, tare da jaddada manufofinta na kara inganta hakkokin mata musamman ma batun zubar da ciki, a yayin da Donald Trump ya ci gaba da mayar da martani a gangaminsa na jihar Arizona.