1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Harris ta samu maki hudu kan Trump a muhimman jihohi

August 11, 2024

Jaridar New York Times da kwalejin Siena sun wallafa cewa mataimakiyar shugaban Amurka kuma 'yar takarar shugabancin kasar a Democrate Kamala Harris, na kan gaba a jihohin Wisconsin da Pennsylvania da kuma Michigan.

https://p.dw.com/p/4jKtW
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris
Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris Hoto: Darron Cummings/AP/picture alliance

Harris dai na gaban Trump da kaso 4 bisa 100 a wadannan jihohi guda uku, tsakanin kashi 50% zuwa 46 bisa 100, wanda hakan ke kunshe a cikin daftarin rahoton kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a ranakun 5 zuwa 9 ga watan Augusta.

Karin bayani: Walz zai mara wa Harris baya

Tun da fari dai, rawar da gwamnatin Biden ke takawa a yakin Gaza ya fusata galibin al'ummar jihohin musamman a Michigan da ke da yawan Amurkawa-Musulmi da kuma Amurkawan da ke da tsatso da Larabawan yankin Gabas ta Tsakiya.

Labarai cikin hotuna:

Shugaba Biden dai ya dankwafar da bukatar tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba, inda ya mika ragamar takarar ga mataimakiyarsa Kamala Harris.