Hasken kafa gwamnati ya bayyana a Jamus
January 12, 2018Shugabar gwamnati Angela Merkel da shugaban jam'iyyar SPD Martin Schulz sun sanar a birnin Berlin cewa sun cimma matsaya ta fara tattaunawa a hukumance don kafa gwamnatin kawance. Tuni ma dai wasu majiyoyin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel suka ce shugabar gwamnatin na son a kammala tattaunawar kafa kawancen da SPD kafin tsakiyar watan Fabrairu.
Ba wata alamar annuri a fuskokin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da jagoran jam'iyyar SPD Martin Schulz lokacin da suka bayyana gaban 'yan jarida da sanyin safiyar ranar Juma'a. Merkel ta yi bakin kokarinta wajen tabbatar wa Jamusawa cewa yarjejeniyar tana kan kyakkyawar turba:
"Jam'iyyar CDU gaba daya ta amince da wannan takarda, wato sakamakon jerin tattaunawar da muka yi, wanda da yawa a cikinmu suka shiga ciki. Mun dogara da ilahirin wakilanmu. Saboda haka muna ba da shawara da a fara tattaunawar kulla kawance da ke da burin kafa gwamnati mai karfi."
Jamus ta kwashe fiye da kwanaki 100 ba ta da gwamnati lamarin da ya sa da yawa daga cikin 'yan kasar ke kara nuna gajin hakuri. Sai dai jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da jam'iyyar SPD ta Martin Schulz ba su yi wani dokin shiga sabon kawance ba. Dukkan sassan biyu sun yi kokarin amincewa da sauye-sauye na siyasa a cikin shekaru hudu da suka wuce, kuma shugaban SPD Martin Schulz ya amsa cewa an sha wuya kafin cimma wani daidaito a wannan karo:
"Yayin tattaunawar mun gane cewa mu jam'iyyu mabambamta, manufofinmu sun bambamta haka nan ma irin aikace-aikacenmu. Burin wannan yunkuri na kulla kawance shi ne a cimma wani daidaito da jam'iyyun biyu za su na'am da shi, wanda kuma zai zama mai amfani ga 'yan kasarmu da kuma masu kada kuri'a na wannan kasa."
Dukkan sassan biyu sun fito da wani kundi mai shafuka 28 kan sabon kawancen. Sai dai yarjejeniya ba za ta yi wa da dama na membobin jam'iyyun dadi ba. CDU da SPD sun amince da wani shirin mayar da makarantu da jami'o'i kan turbar fasahar digital da sauye-sauye a tsarin kiwon lafiya da karancin kudin fansho ga talakawan kasa. Amma dukkan biyu sun yi fatali da wasu alkawuran zabe da suka dauka.
Tuni dai kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da daidaiton da aka cimma tsakanin manyan jam'iyyun na Jamus kan fara tattaunawar kafa gwamnatin kawance.