Hatsarin jirgin sama a Legas
October 3, 2013Mahukunta sun ce wani jirgin sama na hayar da ke ɗauke da passinjoji 20 ya faɗi ya kama da wuta jim kaɗan bayan tashiwarsa daga filin jirgin saman Lagos dake Najeriya.
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya rawaito ce aƙalla mutane15 suka rasa rayukansu.
Mai magana da yawun hukumar kula da jiragen saman na tarayya Yakubu Datti ya ba da tabbacin cewa mutane biyar sun rayu a hatsarin kuma an garzaya da su asibiti.
Yawancin kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ce jirgin na ɗauke ne da iyalai da kuma gawar tsohon gwamnan jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar wato Olusegun Agagu wanda za a je janaizar sa.
Kwamishinan 'yan sanda Sanau Waheed, wanda ya zanta da manema labarai ya ce an yo hayar jirgin ne daga kamfanin Associated Airline daga jihar Legas zuwa jihar Ondo kuma ya yi saukar gaggawa a ɗaya daga cikin tsoffin shingayen da ake karɓar kuɗi a hanun masu ababen hawa, wanda ke kusa da wurin ajiyar man fetur.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal