Hatsarin jirgin sama a Namibiya
November 30, 2013Kamfanin dillancin labaran kasar Namibiya ya ruwaito cewar, wani jirgin samam mallakar kasar Mozambik yayi hatsari a yankin arewa maso gabashin kasar, inda kuma ya janyo mutuwar daukacin fasinjoji 34 da ke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran ya ambaci wani jami'in dan sanda a kasar yana cewar, babu wanda ya tsira da ransa yayin hatsarin jirgin saman da ya afku - wannan Asabar (30.11.30), a Namibiya. Dama dai jirgin, kirar TM470, ya taso ne daga birnin Maputo, na Mozambik inda yake kan hanyarsa ta zuwa Luanda, babban birnin kasar Angola. Akwai dai fasinjojin da yawansu ya kai 28 a cikin jirgin, da kuma ma'aikata shida.
Bollen Sankwasa, mukadashin kwamishinan kula da harkokin 'yan sanda a yankin Zambezi na Namibiya, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar cewar, jirgin ya tarwatse ne a gandun dajin Bwabwata dake yankin arewa maso gabashin kasar. Jiragen saman kamfanin LAM, kamar dai sauran jiragen saman kasar ta Mozambik, an haramta musu yin zirga zirga a sararin samaniyar kasashen Tarayyar Turai saboda rashin cika ka'idojin da Kungiyar Tarayyar Turai ta gindaya dangane da sufurin jiragen sama.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman