Hatsin Rasha ga kasashen shida na Afirka
February 21, 2024Ma'aikatar aikin gona ta Rasha ta bayyana kammala shirin tura kimanin hatsi ton-dubu-200 zuwa kasashen Afirka guda shida kyauta, kamar yadda Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha ya yi alkawarin ga shugabannin kasashen a shekarar da ta gabata.
Ministan ma'aikatar noma Dmitry Patrushev na kasar ta Rasha ya tabbatar da haka a wani sakon da aka wallafa a wannan Talata da ta gabata, inda kasashen Somaliya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kowacce za ta samu ton dubu-50, kana sauran kasashen Mali da Burkina Faso, da Zimbabuwe da Eritrea kowacce ton dubu-25.
Matakin yana cikin shirin Rasha na rage radidnin yaki da ke faruwa tsakanin kasar da Ukraine, abin da ya haifar da tsadar hatsi, kuma lokacin ganawa da shugabannin na Afirka ne gwamnatin ta Rasha ta yi alkawarin ba da taimakon ga kasashen kyauta.