Matshiya mai sana'ar sayar da abinci
December 22, 2021Matashiyar mai suna Balkissa Hamidou Alkali ta kafa masana'antarta mai suna Kissa Jus et Confisseries, inda take sarrafa abinci kala-kala da kayan marmari da kayan sanyaya rayuwa daga albarkatun noma da kiyo irin namu na gida domin dogaro da kai. A cewar Matashiyar mafarkinta ne ya zamo gaskiya. Sannu a hankali dai masana'antar tata tana samun karbuwa a takanin al'umma, sai dai akwai kalubale mai yawa musaman rashin tallafi da harajin da ake tsawwala mata.
Ma'aikatu da kamfanoni da ma sauran al'umma masu shagulgulan aure ko suna ko wani taro, na hulda da masana'antar Kissa Jus ta Bakissa Hamidou Alkali kuma suna yabawa matashiyar a kan himmarta da kokarinta. Koda yake tana mace matashiyar ba ta yi kasa a gwiwa ba wurin neman na kanta, hakan yasa danginta mata ke jinjina mata.
Matasa hudu ne 'yan mata biyu da samari biyu ke tallafawa matashiyar wurin aikace-aikacen masana'antar, kuma suma daga nasu bangare sai dai godiya saboda rufin asirin da suke samu karkashinta. Himma dai ba ta ga raggo, burin matashiyar shi ne na kafa kamfanin horar da matasa girke-girken abinci, saboda haka ta yi kira ga 'yan uwanta matasa su tashi su rungumi sana'o'in dogaro da kai maimakon jiran aikin gwamnati da babu tabbas.