Matashiya ta samar da manhaja
March 17, 2021Yanzu haka dai matashiya dai ta zama tauraruwa a yankin arewacin Najeriya, sakamakon kirkirar wannan manhaja. Sa'ada Aliyu na kiran manhajar mai fallasa wadanda suka aikata laifukan fyade da "Helpiyo." Manhajar na taimakon hukumomi da kungiyoyin da za su kai dauki ta hanyar fallasa masu wannan muguwar dabi'a. Haifaffiyar jihar Kano, Sa'ada Aliyu ta yi karatunta ne a fannin kimiyar Computer.
Bisa al'ada dai ba kasafai ake iya cimma nasara ba tare da kalubale ba, dan haka matashiyar ta bayyana cewa duk da tarin nasarori da ta cimma, ta kuma fuskanci wasu kalubale kan wannan manhaja. Haka kuma Sa'ada ta bayyana matukar takaici kan yadda ake aikata fyade ba tare da an bi wa wadanda aka yi wa hakkinsu ba. A karshe Sa'ada Aliyu ta zaburar da matasa kan su dukufa wajen amfani da iliminsu, domin samar da hanyoyin ci-gaba ga al'ummar su, tana mai cewa matasa sune kashin bayan kowacce alumma.