Hezbollah na kan gaba a zaben Lebanon
May 7, 2018Rahotanni daga wasu kafofin yada labaran Lebanon na nuni da cewa kungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan kasar Iran, na kan gaba da yawan kuri'u a zaben 'yan majalisun dokoki da aka gudanar. Sai dai alkaluma sun nuna cewa kashi 49 cikin 100 na 'yan kasar ne suka fito kada kuri'unsu.
Kujeru 128 ne ke fatan samun wakilci daga sassa daban-daban, amma zaben ya fuskanci korafe-korafe na rashin ba dai-dai ba a wasu wurare. Ma'aikatar cikin gida na danganta matsalar da aka samu da sauye-sauyen tsarin gudanar da zaben.
Kawo yanzu ba a tabbatar da sakamakon zaben a hukumance ba, amma masana na ganin zaben ba zai raba gardama tsakanin kungiyoyn addinai da ke sa'insa a kasar ba, inda ake ganin Firaiminista Sa'ad Hariri da ke samun goyon bayan Saudiyya zai iya sake kafa gwamnati a Lebanon.