1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton ta yi nasarar kafa tarihi

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 27, 2016

Jam'iyyar Democrat ta amince Hillary Clinton ta zama mace ta farko 'yar takarar shugabancin Amirka a zaben da zai gudana a ranar 8 ga watan Nowamba.

https://p.dw.com/p/1JWO7
USA Wahlen Parteitag der Demokraten in Philadelphia Hillary Clinton
Hoto: Reuters/M. Kauzlarich

Hillary Clinton ta yi nasarar kafa tarihi a Amirka, inda ta zama mace ta farko da aka tsayar a matsayin 'yar takara a zaben shugaban kasa. Ita dai mai dakin tsohon shugaba Bill Clinton kana tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amirka ta samu tsayawa ne karkashin tutar jami'ar Democart a lokacin babban taro da ya gudana.

Cilton Za ta kara da dan takara Donald trump na jam'iyyar Republican a zaben da zai gudana a ranar 8 ga watan Nowamba mai zuwa. Sai dai kididdigar jin ra'ayin jama'a na baya-bayannan da aka gudanar ya nunar da cewar abokin hamayyarta ya zartata a farin jini.