Hillary Clinton ta ziyarci Sudan ta Kudu
August 3, 2012A yau Juma'a ne sakatariyar harakokin wajen Amirka Hillary Clinton, ta kai wata ziyara a sabuwar kasar Sudan ta Kudu a rangadin da ta fara a Afrika, inda za ta gana da shugaba Salva Kiir a kan wasu muhimman batutuwa ciki har da batun gaugauta samun daidaito da makwabciyar kasar Sudan ta shugaba Albashir a kan rikicin kan iyaka da na ma'adanun man fetur.
A jiya ne a ka kai karshen wa'adin biyu ga watan Augusta da Majalissar Dinkin Duniya ta baiwa kasasahen biyu na su cimma yarjejeniya a kan batutuwan da suka haddasa rikicin.
To saidai kawo yanzu kasashen guda biyu sun kasa samun daidaito a tautaunawar da suke yi a karkashin jagorancin kungiyar gamayar Afrika ta AU.
A shekarar bara ne dai kasar ta Sudan ta Kudu ta samun 'yancin gashin kanta daga Sudan bayan kazamin yakin da a ka share shekaru sama da 25 suna gobzawa.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Abdullahi Tanko Bala