1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hira da Angela Merkel

Zainab A MohammedJanuary 14, 2007

Shekaru 50 bayan kafuwar KTT,jamus na shugabanci

https://p.dw.com/p/BvR7
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AP

Kasancewar jamus ta karbi madafan ikon gamayyar kasashen turai na tsawon watattani da kasashe masu cigaban masanaantu na G8 daga watan janairun wannan shekara,shugabar gwamnatin Angela Merkel ta bayyana manufofinta na hadin kai da sauran kasashe wajen yakar harkokin masu tsananin raayi, ahiran datayi da gidan Ragion DLF,kamar yadda zainab Mohammad Abubakar ta fassara.......

Ina da hakki daya rataya a wuyan,wannan kuma hakki ne daya rataya a wuyan gwamnatina baki daya ,babu yadda zamu cimma nasa a wadannan manufofi namu da muka sanya gaba ba tare da hadin kai ba.

Dole ne muyi nazari kann wadannan matsaloli,da kuma yadda zamu kalubalanci wannan matsala domin gamno baki zaren warware shi.Wannan kuma matsala ce da gwamnati na dani kaina zamu iya aiwatar dasu kadai idan munsanya a zukatanmu cewa,hakki ne daya wajaba akammu .

Dayake waddana matsaloli ne da zaa iya cewa masu nayuyin gaske musamman wajen tinkarasu,a matsayin na shugabar kasa,ko kina da wata madafa?......

"Ai daman haka yake idan sauran kasashe wakialai suna sane da matsalar dake da akwai domin tunkara,zan sake nanata cewar kamar batu na samar da makamashi ko kuma harkokin gudanarwa,ya zamanto wajibi a samu hasdfin kai wajen samo bakin zaren warware shi .Kuma Siyasa na muradin tubali ne,inda zaa dora akai domin samun cigaba da nasara,kuma kowane shugabanci yana bukatar shawarwarri daga kowane bangare,wanda zaiyi nazari akai.

Wannan kungiya ta tarayyar turai dai ta fara ne da wakilcin kasasdhje shida a shekaru 50 da suka gabata a birnin Rome din kasar Italia,ayabzu kuwa da hadewar Rumenia da Bulgeri a wannan shekaru tana da wakilai 27 kenan,bazaa iya cewa yanzu kungiyar ra rataye da babban nauyi ba?...

Babu ko kadan,Turai baki dayanta nada nasarori a tarihinta.Kasashe shidan da suka fara ta sun kasance masu dogaro akan juna ne ta bangarori daban daban,saboda ta haka ne suka kirkiro wannan gamayya.Kasashe basu da wani haufi akan junansu,sai dai sukan amincewa juna fadada harkokin kasuiwanci ta hanyar bawa kowace kasa ikon shigar da kayayyakinta.Kuma hakan ya jagoranci babban nasara a bangaren wakilan kasashe.Kamar yadda ayau zaa iya ganin misali a dangantakar wadannan kasashe namu da Amurka.

......